Girgizan kasa mai karfin ma’aunin Richter 4.1 da ta faru a garin Bam da kewaye a cikin lardin Kirman a nan kasar Iran a safiyar yau Litinin da misalign karfe 8:15 na safe, bai zo da wata asara ba.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban twagar kungiyar bada agaji ta Hilal Ahmar ko (Red Cross) kamar yadda aka sanshi a sauran kasashen duniya yabayyana cewa, tawagar tasa ta zagaya cikin garin da kuma kauyukan da suke kewaye da shi sun kuma gano cewa babu wani barnan da ta yi.
Reza Fallah jami’an hulda da Jama’a na kungiyar ya bayyana cewa sun aike tawagar yan agaji har guda biyu zuwa yankin bayan da suka sami labarin awkuwar girgizan kasar ya ce sun zagaya cikin garin bam da kuma dukkan kauyukan da suka tasirantu ko suka ji karar girgizan kasar, basu ga wata barna ta rai ko dukiyan da ta jawo ba.
A safiyar yau litinin 2 ga watan Nuwamba shekara ta 2026 ne, da misalan krfe 8:39 aka fara wata girgizan kasa mai karfin ma’aunin rechter 4.1 . Ya ce girgizab kasar tana da zurfin kilomita 15, sannan yana da fadin kilomita 58.32 mai nisan kilomita 4 daga garin Bam.