Gina Tsaro Kan Tsoma Bakin Kasashen Waje Ba Zai Yi Karko Ba

iran tayi nasara kan kasar Amurka da isra'ila ne saboda hadin kai da juriya

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqer Qalibaf ya bayyana cewa hadin kai da ake da shi tsakanin alummar musulmi ya yi galaba kan makircin makiya, ya jaddada cewa tsaron yankin da ya dogara a halin yanzu da  tsoma bakin mabota girman kai na duniya wanan yasa  ba zai yi karko ba.

A cikin sakon da ya aike da shi kan makon hadin kai Qalibaf yace iran kasa ce mai son zaman lafiya tsakanin kungiyoyi da kabilu da alummomin musulmi, yace rera taken hadin kai tsakanin shia da sunna yana da muhimmancin sosai.

A yau hadin kai tsakanin shia da sunna a iran bai zamo kamar wani take ba ne , yana daya daga cikin tushen ikon kasa kuma daya daga cikin manyan kadarorin kasa na samar da tsaro da kuma ci gaba, kuma yayi ishara game da hadin kai da aka samu tsakanin mabanbanta addini a lokacin yakin farko da na biyu da na ukku yace dukkan alumomi sun mike tsaye wajen tunkarar makiya kasar iran dake kasashen waje.

Daga karshe Qalibaf ya ce duniyar musulmu yanzu tana fuskanta wani zabi na tarihi , ya  ce abubuwan da suka faru a yankin a yan shekarun nan suna nuna cewa kasashen musulmi da gwamnatoci suna kara fahimtar cewa kasashen waje da makiya musulunci ba zasu iya samar da tsaro mai dorewa ba a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted