Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran sharia da kuma na kasa da kasa, Kazim Gharib Abadi ya bukaci hukumar yaki da hana amfani da makaman guba a duniya kada ta shigar da siyasa a ayyukanta.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Gharib abadi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabata a jiya Litinin a taron hukumar ta CEC karo na 29 a birnin Haque na kasar Nethalands.
Ghariba Abadi ya kara da cewa matsayin JMI dangane da makaman guba a fili yake.
Ya kuma kara da cewa JMI itace kasa wacce tafi cutuwa da makaman guba a wannan zamanin, saboda yadda aka yi amfani da makaman guba a kan mutanen kasar Iran a yakin shekaru 8 da ta fafata da gwamnatin kasar Iraqi ta lokacin.
Mataimakin ministan ya yi kira ga kasashen yamma su dakatar da tallafin da suke bawa HKI a kissan kare dangin da take yi a gaza.