Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fuskanci Mummunan Martanin Soji

Babban Hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya gargadi Haramtacciyar Kasar Isra’ila da kuma Amurka kan cewa duk wasu hare-hare kan kasar zai kara fushin sojojin

Babban Hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya gargadi Haramtacciyar Kasar Isra’ila da kuma Amurka kan cewa duk wasu hare-hare kan kasar zai kara fushin sojojin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan sojojin sama na Iran Major General Abdolrahim Mousavi yana fadar haka a lokacin ganawarsa da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Afrika ta kudu General Rudzani Maphwanya a yau talata a nan Tehran.

Janar Mousavi ya kara da cewa dakarun kare juyin juta halin musulunci a nan Iaran wato IRGC sune sojojin da suka fi kawo fada da yan ta’adda a duniya, sannan rundunar a shirye take ta yi aiki da sojojin Afrika Ta Kudu don samun irin kwarewan da rundunar take da shi a wannan bangaren a kuma sauran bangarori.

Ya kuma kara da cewa duniya taga yadda dakarun na IRGC suka maida martani kan HKI da kuma Amurka a yakin da suka dorawa kasar a kwanaki 12 a cikin watan yunin da ya gabata.

A wani bangaren babban kwamandan sojojin sama na dakarun IRGC ya bayyana cewa kasashen yamma musamman Amurka da HKI ba sa da alkawali, don haka zasu iya karya alkawalin da suka dauka da kowa a ko yauce idan sunga zasu sami biyar bukata.

Daga karshe Mousavi ya yabawa kasar Afirka ta kudu da gabatar da HKI a gaban kotun ICC saboda ayyukan kissan kare dangi da take aikatawa a Gaza.

A nashi bangaren Janar Maphwanya y ace, dangantaka tsakanin Iran da afirka ta kudu ya samo asali daga goyon bayan da JMI ta bawa gwagwarmayan mutanen kasar don samun yencinsu daga gwamnatin wariyar launin fata. Ya daga nan ne kasashen biyu suka aiki da juna a banari da dama daga ciki har da bangaren tsaro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted