Iran: Duk Kasar Da Ta Goyi Bayan Amurka Wajen Kai Mata Hari To Za ta Kai Mata Hari

kasar iran ta ce duk kasar da ta goyi bayan amurka wajen kai mata hari to za ta kai mata hari

Mai bawa kwamandan dakarun kare juyin musulunci na kasar iran yayi gargadin cewa duk wata kasa data taimakawa kasar Amurka a wani sabon hare haren da za ta kai wa iran to za ta dauketa a matsayin abokiyar gaba da ta halasta a kai mata hari

Birgadier janar Ali Belali yayi wannan bayanin ne a hira da yayi da gidan talabijin din al’alam dake watsa shirye shiryensa da harshen larabci bayan da jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah sayyid mujtaba Khamena’i ya bada umarni ga kamwadojin soji na kasar su tabbatar sun mayar da martani ga duk wani hari, ba tare da la’akari da wata iyakar taswirar kasa ba

Ya kara da cewa duk wasu sojoji ko kuma kasa da ta taimakawa Amurka wajen kai mata hari to daga lokacin sun zama nama da za ta kai musu hari, hakika wannan ya dogara ne kan kasar da ake Magana akai, da kuma matakin da take dauka wajen yin hadin guiwa da kuma daidaita ayyuka tare da Amurka

Daga karshe kuma ya jaddada cewa zaa bayyana jerin sunayen abubuwan da iran tasa a gaba lokacin da ya dace wato duk lokacin da makiya suka sake yin kuskuren sake jefa kasar cikin wani sabon yaki

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted