Iran: Dole Ne Amurka Ta Aiwatar Da Yarjeniyar Islamabad

Wani babban jami’an diblomasiyya na kasar Iran ya bayyana cewa dole ne gwamnatin kasar Amurka ta aiwatar da yarjeniyar da aka cimma da ita a

Wani babban jami’an diblomasiyya na kasar Iran ya bayyana cewa dole ne gwamnatin kasar Amurka ta aiwatar da yarjeniyar da aka cimma da ita a birnin Islamabd a farkon wannan shekara. bayan yakin kwanaki 40 da ta dorawa kasar.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehra ta nakalci Kazem Gharib Abad mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a al-amuran sharia na kasa da kasa yana fadar haka a yau Lahadi.

GharibAbadi ya bayyana haka ne a lokacinda yake amsa tambayoyi dangane da ziyarar da jami’an gwamnatocin kasashen Pakistan Qatar da kuma Omman suka kawo nan Tehran a makon da ya gabata.

Yace : Iran bata fara yaki da AMurka da HKI ba, don haka ba wanda ya isa ya ce tana da laifi wajen kare kanta, bata bar makiyanta suka mamayeta ba. Ya bukaci Amurka ta aiwatar da dukkan abinda aka cimma da ita a yarjeniyar Islamabad kafin Iran ta aiwatar da abinda suka cimma da kasar Omman na yanda zirga zirgan jiragen ruwa zasu kasance a mashigar ruwa ta Hurmuz.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted