Shugaban kasar Iran ya jaddada aniyar kasarsa ta zurfafa dangantakarta da Uzbekistan tare da kyakkyawar manufar juna
Shugaban Kasar Iran Mas’oud Pezeshkian da takwaransa na Uzbekistan Shavkat Mirziyoyev sun jaddada dangantakar abokantaka da ta ‘yan’uwantaka tsakanin Iran da Uzbekistan da kuma bukatar amfani da albarkatun da ake da su don zurfafa dangantaka da kuma bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban.
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Shugaba Pezeshkian ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Uzbekistan Shavkat Mirziyoyev a ranar Talata da rana, inda suka tattauna sabbin ci gaban da aka samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma hanyoyin bunkasa da kuma karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.
A tattaunawar, shugaban ya jaddada dangantakar ‘yan’uwa da abokantaka tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Uzbekistan, yana mai cewa: “Ya fi muhimmanci fiye da kowane lokaci a zurfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma fadada alaka tsakanin al’ummomin biyu a fannoni daban-daban ta hanyar hadin gwiwa da kuma ra’ayi daya.”
Shugaba Pezeshkian ya yi tsokaci kan muhimmancin haɓaka dangantaka da ƙasashen da ke makwabtaka da juna a cikin manufofin harkokin wajen kasar Iran, yana mai cewa “faɗaɗa dangantaka da ƙasashe daban-daban, musamman ƙasashe masu abokantaka waɗanda ke kusa da Iran a matsayin babban manufofin da Iran ta fi mayar da hankali a kansa.