Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun yi kira da babbar murya da a kare martabar kasa da kuma yankin kasar Siriya tare da dakatar da hare-hare da Isra’ila ke kai wa kasar.
A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da yammacin jiya Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi da takwaransa na kasar UAE Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan, sun yi nazari kan al’amuran baya-bayan nan a kasar Siriya bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad.
Araghchi da Al Nahyan sun tattauna kan mahimmancin kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da kuma kaucewa duk wani mataki na tunzura jama’a da zai iya dagula hadin gwiwa a tsakanin kasashen yankin a halin da ake ciki.
Tun bayan kifar da gwamnatin Assad, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hare-hare ta sama kusan sau 500 a duk fadin kasar ta Siriya, inda ta lalata muhimman ababen more rayuwa na fararen hula da kayayyaki na soji.
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kuma tura dakarunta zuwa wani yankuna na kasar Syria tare da mamaye wadannan yankuna, wanda kuma hakan ya saba wa yarjejeniyar shekarar 1974.
Isra’ila ta kuma aike da dakaru zuwa wani yanki da ke gabashin da tuddan Golan da ta mamaye.
Ministocin biyu sun kuma yi tsokaci kan muhimmancin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya baki daya.