Iran Da UAE Sun Tattauna Alakar Dake A Tsakaninsu

Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da na Hadaddiyar Daular Larabawa sun tattauna kan dangantakarsu da halin da ake ciki a yankin. Ministan harkokin wajen Iran Abbas

Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da na Hadaddiyar Daular Larabawa sun tattauna kan dangantakarsu da halin da ake ciki a yankin.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Abdullah Bin Zayed Al Nahyan sun gana ne a birnin Dubai ranar Lahadi.

An gudanar da taron ne bisa gayyatar Al Nahyan yayin da Arakchi ke kan dawowa gida daga ziyararsa ta farko a kasar Sin tun bayan zama ministan harkokin wajen Iran.

Ministocin biyu sun yi musayar ra’ayi game da hanyoyin inganta alaka a fannoni daban daban da kuma halin da ake ciki a yankin.

Dama a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar 12 ga watan Disamba, Araghchi da Al Nayhan sun tattauna kan lamuran da ke faruwa a Siriya bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad.

Sun yi kira da kakkausar murya da a kare ‘yancin kai na kasar Syria tare da dakatar da hare-haren da Isra’ila ke yi wa kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments