Kasashen Iran, Rasha, Azerbaijan, da kuma Kazakistan sun rattaba hannu kan yarjeniyar samar da tsaro a ruwayen tekun Caspian wadanda suke tarayya a mallakarsu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kwamandojin sojojin ruwa na wadannan kasashe sun rattaba hannu a kan yarjeniyar a yau Laraba a birnin St. Petersburg na kasar Rasha.
Kuma sun kara jaddada cewa ba zasu taba amincewa wata kasa a duniya ta shiga yankin da sunan tsaro ruwan tekun ba.
Rear Admiral Shahram Irani, babban kwamandan sojojin ruwa na JMI ne ya wakilci JMI a bikin rattabawa yarjeniyar hannu. Ya kuma bayyanawa kafafen ya da labarai kan cewa manufar yarjeniyar ita ce takaita tsaron ruwan tekun Caspian a tsakanin kasashen da suke bakin ruwan tekun kadai.
Shahran Irani ya ce ‘wannan ruwan mallakin kasashe biyar ne, don haka nauyin kula da shi yana hannun wadan nan kasashe ne kadai, babu wata kasa daga cikin yankin ko kuma wani wuri, ke da hakkin kula da tsaronsa sai wadannan kasashe 5.