Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Alakarsu  A Fagen Shari’a

Ministan harkokin shari’a na Iran  Amin Husain Rahimi ya bayyana alakar dake tsakanin kasarsa da Saudiyya da cewa tana da matukar muhimmanci, tare da jaddada

Ministan harkokin shari’a na Iran  Amin Husain Rahimi ya bayyana alakar dake tsakanin kasarsa da Saudiyya da cewa tana da matukar muhimmanci, tare da jaddada muhimmancin bunkasa ta a fagen shari’a.

A jiya Lahadi ne dai jakadan Saudiyya dake nan Iran  Abdullah Bin Sa’ud al-Anzi ya ziyarci ma’aikatar shari’a inda ya gana da ministan shari’a Amin Husain Rahimi.

Ministan na Iran ya yi ishara da kokarin da wannan gwamnatin ta Mas’ud Fizishkiyan take yi na siyasar bunkasa alaka da dukkanin kasashen makwabta a cikin fagagen al’adu, tattalin arziki, siyasa da kuma shari’a.

 Tun a farkon ziyarar, jakadan kasar Saudiyya a Iran din, Abdullah Bin Sa’ud al-Anzi, ya bayyana gamsuwarsa da yadda alaka a tsakanin kasashen nasu take tafiya.Haka nan kuma ya mika sakon gaisuwa daga ministan harkokin shari’a na Saudiyya.

Jakadan na Saudiyya ya kuma bayyana fatansa na ganin cewa an bunkasa alakar kasashen biyu ta fuskar shari’a domin kai ta zuwa wani matsayi na koli.

Bayan ganawar, jakadan na Saudiyya ya bayyana cewa ta kasance mai matukar muhimmanci, sannan kuma ya yi fatan ganin na cigaba da bunkasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments