Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin

Kasashen Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan hadin kan Musulmi game da halin da ake ci a yankin Wannan bayannin ya fito ne a

Kasashen Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan hadin kan Musulmi game da halin da ake ci a yankin

Wannan bayannin ya fito ne a yayin ganawar sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani da yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Mohammed bin Salman a birnin Riyadh inda suka tattauna kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin.

Ganawar dai ta nuna wani muhimmin mataki a huldar diflomasiyya ta tsakanin Tehran da Riyadh.

Larijani ya tafi Saudiyya ne bisa gayyatar da ministan tsaron kasar ya yi masa, inda ya jagoranci tawagar da ta hada da mataimakin sakataren harkokin kasa da kasa Ali Bagheri Kani da mai ba da shawara kan harkokin yankin Gulf na Farisa Mohammad Ali Bek.

Ganawar na zuwa ne kwana guda kacal bayan da shugaba Masoud Pezeshkian ya gana da bin Salman a gefen taron gaggawa na kasashen Larabawa da Musulunci da aka yi a birnin Doha, inda bangarorin biyu suka nuna gamsuwarsu da yadda huldar dake tsakanin kasashen biyu ke kara habaka.

Ziyarar Larijani a Riyadh ita ce ziyararsa ta uku a yankin tun bayan hawansa mulki a ranar 5 ga watan Agusta, biyo bayan ziyarar da ya kai a Iraki da Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted