A wata ziyarar da wata tawagar yan jarida daga Iran suka kai birnin Mosco, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin habaka dangantaka na sardarwa tsakanin kasashen biyu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa hukumar tashoshin talabijin da Radiyo na kasar Iran da kuma na bangaren Rasha sun karan zurfafa dangantaka tsakaninsu a fagen yada labarai a yankin da kuma duniya gaba daya.
Labarin ya kara da cewa wannan dangantakar zai sa fuskance labaran karya wadanda kafafen yada labarai na yamma suke yadawa.
Har’ila yau yarjeniyoyin aiki tare tsakanin hukumomin watsa labaran kasashen biyu zai samar da labarai iri guda da kuma fadada hanyoyin samun labaran gaskiya a tsakaninsu.
Daga cikin yarjeniyoyin dai akwai na tsakanin tashar talabijin ta Presstv da Presstv da labaran bidiyo na Ruptly wanda Ahmad Nourozi na Presstv da shugaban labaran bidiyo na kasar Rasha. Hakama BRICS Tv da IRIB da kuma Zvezda Tv, Na kasar Rasha.