Iran Da Rasha Zasu Gina Cibiyoyin Makamshi Nukliya

JMI nan ba da dadewa ba zata sanya hannu a kan yarjeniyar fahintar juna da kasar Rasha don gaggauta gina kananan cibiyoyin samarda wutan lantarki

JMI nan ba da dadewa ba zata sanya hannu a kan yarjeniyar fahintar juna da kasar Rasha don gaggauta gina kananan cibiyoyin samarda wutan lantarki na makamashin nukliya, a kasar wansa ake kira (SMRs).

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar  iran ya nakalto kakakin hukumar makamashin Nukliya na kasar Iran yana fadar haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa. Iran tana kara fadada shirinta na makamashin Nukliya da gaggawa kuma shirin zai ci gaba duk tare da gaban da HKI da Amurka suke yi da shi.

Behrouz Kamalvandi kakakin hukumar makamashin nukliya ya bayyana haka ne a yau a birnin Seoul babban birnin kasar Korea ta Kudu inda ake gudanar da taron ministocin kasashe masu son bunkasa amfani da makamashin nukliya a duniya.

Yace gurbatar yanayi da matsalolinta sun bayyana ga kowa a duniya, ya kuma karfafa amfani da makamashin nukliyar don fuskanta da kuma magance matsalar.

Yace a halin yanzu ana samar da megawatts 400,000 na wutan lantarki a duniya gaba daya, sannan kasar Iran tana da kimani megawatts 1000 daga ciki.

Kamalvandi ya kara da cewa a cikin wannan shirin Iran zata kara gina cibiyoyin bada wutan lantarki tare da amfani da makamashin nukliya mai karfin megawatts 1,200 wanda za’a kwatantashi da wacce ake da shi a birnin Bushar na kudancin kasar Iran.

Kakakin hukumar ta AEOI ya ce, ci gaban da ake samu a kirkirerren fasaha ko AI, da ci gaba a ababen hawa masu amfani da lantarki da ci gaban fasahar amfani da lantarki a al-amura da dama, sun sa samar da shi ya zama wajibi.

Yace samar da SMRs wato kananan cibiyoyin bada wutan lantarki yana kara samun karbuwa a duniya, kuma da hakan ana iya magance matsalolin karancin wutan lantarki a duniya. Daga karshe yace, Iran zata sanya hannu tare da kasar Rasha don samar da wutan lantarki tar

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted