Gwamnatin kasar Iran da Rasha zasu gaggauta aiki tare a bangaren makamashi don fuskantar takunkuman man fetur wanda Amurka ta dorawa kasar.
Kamfanin dillancin labaran FarsNews ya bayyana cewa kasashen biyu zasu yi haka ne ta kwamitin hadin giwa na tattalin arzikin da ke tsakanin kasashen biyu.
Labarin ya kara da cewa, ministocin man fetur na kasashen biyu sun bayyana haka a taron kwamitin hadin giwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
Gwamnatin Amurka dai ta dorawa Rasha da Iran takunkuman saida danyen man fetur na kasashen biyu. Sannan. A halin yanzu dai gwamnatin shugaba Trump tana fama da matsalolin tsadar makamashi a duk fadin Amurka saboda rufe mashigar ruwa ta Hurmuz wanda sojojin kasar Iran suka yi tun ranar da Amurka da HKI suka farwa kasar da yaki a ranar 28 ga watan Fabrayrun shekara 2026.
Banda haka yawan man fetur da kasar ta ajiye ya ragu zuwa ganga miliyon 284 kacal wanda ba’a taba ganin irin haka ba . Don haka batun neman hanyoyin fadada hanyoyin bunkasa harkokin makamashi tsakanin kasashen Iran da Rasha yana da matukar muhimmanci a wannan lokmaci.