Iran da Rasha Sun yi Watsi Da Kasancewar Sojojin Ketare A Yankin Kafkaz

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a yayin tattaunawarsa da takwaransa na kasar Rasha ya bayyana cewa tabbatar da tsaro a kafkaz da tsakiyar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a yayin tattaunawarsa da takwaransa na kasar Rasha ya bayyana cewa tabbatar da tsaro a kafkaz da tsakiyar Asiya ya doru ne a wuyan kasashen yankin, don haka basu yarda wani daga wajen ya tsoma baki cikin harkokinsu ba.

Yankin Kafkas ya zama cibiyar gasar siyasa a tsakanin kasashen dake fama da rikici tsakanin Rasha da Nato da  Turkiya da kuma kasashen yankin, don haka nuna rashin amincewar iran na shigar da sojojin kasahen waje alama ce ta kokarin iran na tsara tsaron yankin tare da Mosko da kuma dakile tasirin kasashen yamma a kusa da iyakokinta na Arewa.

Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa zaman lafiya da tsaro a kafkaz da tsakiyar Asiya kasashen yankin ne ya kamata su samar da shi, ba tare da tsoma bakin wani daga waje ba, wanda haka ya nuna afili cewa iran tana adawa da kasancewar sojojin ketare a yankin na kafkas kuma ta isar da matsayinta ga makwabta da kuma  kawayenta.

Haka zalika yace iran da rasha sun yi tarayya da fahimtar juna kan wannan batun , inda dukkan bangarorin biyu suka yi watsi da batun shigar wani karfi daga wajen a yankin wajen samar da tsaro a kafkaz.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted