Shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan ya bayyana cewa gaggauta aiwatar da yarjeniyoyin da aka kulla yana daga cikin abin da yake da matukar muhimmana dangantakar dake tsakanin mosko da Tehran, saboda hikimar dake cikin dangantar tana bukatar ci gaba da tuntubar juna da kuma sa ido ga ayyukan hadin guiwa.
Shugaban iran ya fadi haka ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da aka yi a jiya talata tsakanin shugaban rasha vildmir putin da mas’ud pezeshkiya, inda shuwagabannin suka yi bitar kyakkyawar dangantakar dake tsakaninsu, kuma sun mayar da hankali a bangaren sufuri, makamashi da kuma samar da karfin wuta lantarki.
Anasa bangaren shugaban kasar Rasha viladmir putin ya bayyana gamsuwarsa game da yadda dangantar take gudana kuma yayi ishara game da harkokin tattalin arziki a matsayin ginshiki, inda dangantakar kasuwanci ta karu da kashi 10 a watannin goman farko na wannan shekara.
Kana yayi ishara game da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na isra’ila suka yi wa iran kuma ya bayyanata a matsayin wanda aka yi watsi da ita kuma ta yin da na sani.