Iran Da Rasha Sun Tattauna Kan Batutuwan Diflomasiyya

Tattaunawa tsakanin manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Rasha a Moscow Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran kuma Shugaban Cibiyar Nazarin Siyasa da Ƙasashen Duniya, Sa’id Khatibzadeh,

Tattaunawa tsakanin manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Rasha a Moscow

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran kuma Shugaban Cibiyar Nazarin Siyasa da Ƙasashen Duniya, Sa’id Khatibzadeh, ya gana da Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Ryabkov domin tattauna sabbin ci gaban da aka samu a dangantakar ƙasashen biyu da kuma tasirin da harin da Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi wa Iran a yankin da kuma ƙasashen duniya gami da wasu batutuwa da dama da suka shafi kasashen junansu.

Khatibzadeh, wanda ke ziyara a birnin Moscow don halartar taron shekara-shekara na Valdai Club, ya gana da Ryabkov. Bangarorin biyu sun yi bitar sabbin ci gaban da aka samu a dangantakar ƙasashensu da kuma ci gaban yankin da na ƙasa da ƙasa. A yayin taron, Khatibzadeh ya sake nanata matsayin Iran, yana mai bayyana godiyar Iran ga goyon bayan Rasha a dandalin tattaunawa na ƙasa da ƙasa, musamman Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da kuma Hukumar Gwamnonin Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya.

A nasa ɓangaren, kasar Rasha ta sake nanata ta’aziyyarta game da shahadar Jagoran juyin juya halin Musulunci da kuma adadi masu yawa na ‘yan ƙasar Iran, kuma taa yaba da jarumtar kare Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga harin, da kuma diflomasiyyar da Iran ta bi a wannan fage.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted