Iran Da Rasha Sun Rattaba Hannu  Na Aiki Tare Akan Muhimman Ayyuka

A wani yunkuri mai matukar muhimmanci na tarihi, shugabannin Iran Mas’ud Fizishkiyan da na Rasha Vladmir Putin sun rattaba hannu na aiki tare akan muhimman

A wani yunkuri mai matukar muhimmanci na tarihi, shugabannin Iran Mas’ud Fizishkiyan da na Rasha Vladmir Putin sun rattaba hannu na aiki tare akan muhimman ayyuka.

A jiya Juma’a ne dai shugabannin kasashen biyu su ka rattaba hannu akan yarjeniyoyin a fadar Kremlin a birnin Moscow.

Wannan yarjejeniyar dai za ta dauki shekaru 20 ana aiki da ita, kuma ta shafi fagagen ilimin kimiyya,tattalin arziki, kere-kere da kuma musayar al’adu.

Gabanin isowa ga rattaba hannu akan wannan yarjejeniyar dai kasashen biyu sun dauki shekaru uku suna tattaunawa, da musayar ra’ayi akan yadda za ta kasance.

Bayan rattaba hannun za a gabatarwa da majalisun kasashen biyu wannan yarjejeniyar domin amincewa da ita, da hakan zai bayar da damar fara aiki da ita.

Wannan yarjejeniyar dai tana a matsayin wani gagarumin sauyi a cikin siyasar kasa da kasa da zai bai wa Iran damar ci gaba da aiwatar da shirin tattalin arizkinta na turjiya. Ita kuwa Rasha zai ba ta damar karfafa matsayinta a siyasar kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments