Kasashen Iran da Rasha sun jaddada shirinsu na taimaka wa gwamnatin Siriya da sojojin kasar wajen kalubalantar ‘yan ta’adda
Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Arakchi da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov, sun tattauna ta hanyar wayar tarho kan abubuwan da suka faru a Siriya.
A cikin wannan zantawar, bangarorin biyu sun bayyana goyon bayansu ga ‘yancin Siriya da amincin kasar da gwamnatin kasar da sojojinta wajen kalubalantar kungiyoyin ‘yan ta’adda, tare da jaddada wajibcin bibiyar lamarin bisa tsarin aiwatar da Shirin zaman birnin Astana na kasar Kazakhstan da kuma hadin kai tsakanin kasashen biyu. Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Rasha, da Turkiyya a matsayin kasashe uku masu tabbatar da wannan tsari.
Araqchi ya bayyana alhakin da ya rataya a wuyan kasashen duniya wajen tunkarar wannan mummunan lamari na ta’addanci, ya kuma dauki yunkurin baya-bayan nan na kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Siriya a matsayin wani bangare na shirin yahudawan sahayoniyya da Amurka na janyo tabarbarewar harkokin tsaro a yankin yammacin Asiya. Ya kuma jaddada wajabcin kara hada kai da taka tsan-tsan tsakanin Iran, Rasha, da sauran kasashen yankin, musamman kasashen dake makwabtaka da kasar Siriya, domin dakile wannan makarkashiya mai hatsari da tunkarar ayyukan ta’addanci a kasar Siriya da yankin.
A nasa bangaren, a wani bangare na tantance abubuwan da ke faruwa a kasar Siriya, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, ya kuma yi la’akari da cewa, hada kai tsakanin dukkan bangarorin wajen tunkarar ta’addanci, da kuma ci gaba da tuntubar juna tsakanin kasashen biyu, kamar yadda ya dace.