Iran Da Oman Sun yi Kira Ga Mdd Ta Dakatar Da Kisan Gilla Da Isra’la Ke yi A Gaza

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi da kuma Badar al-busaidi sun tattauna ta wayar tarho kan danagantakar dake tsakanin kasashen biyu kuma sun bukaci

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi da kuma Badar al-busaidi sun tattauna ta wayar tarho kan danagantakar dake tsakanin kasashen biyu kuma sun bukaci majaliasar dinkin duniya da ta dakatar da HKI ci gaba da kisan kare  dangi da take yi a yankin Gaza.

Kasashen Iran da Oman suna da tsohuwar danagantaka tsakaninsu kuma yanzu haka sun rattaba hannun kan yarjeniyoyi guda 10 kuma za su yi aiki tare a bangarori daban guda biyar,wadannan yarjeejniyoyi an kulla su da nufin kara karfin dankon zumunci a bangarori daban-daban da suka hada da ilimi  tattalin arziki siyasa lafiya tsaro makamashi fasaha da kuma albarkatun kasa

Daga karshe dukkan kasashen biyu sun tir da hare-haren soji da HKI ke yi a yankin Gaza kuma sun yi kira da a dauki mataken gaggawa domin kawo karshen kisan gilla da HKI ke yi , Kuma sun jadda bukatar hukumta dukkan shuwagabanin Isra’ila dake da hannu kan Taa’sar Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted