ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tuntubi takwaransa na kasar Oman game da batun tattaunawa da za’a yi ba ta kai tsaye ba tsakaninta da kasar Amurka
babban jami’an diflomasiyar yayi Magana da Badr bin Hamad Al-Busaidi ne ta wayar tarho a yau litinin inda suka tattauna da kuma musayar ra’ayi game da matsayinsu game da tattaunawa ba ta kai tsaye ba da suke yi da Amurka.
tun da fari dai ministan harkokin wajen kasar Oman ya nuna gamsuwa da goyon bayan sa ga tattaunawar kuma ya tabbatar da cewa tattaunawar karo na ukku zata wakana ne a ranar Alhamis mai zuwa tsakanin Iran da Amurka a birnin Janeva
tun a ranar 6 ga watan Fabareru ne Tehran da washington suka tattauna zagaye na biyu bisa shiga tsakanin kasar Oman kan shirin ta na nukiliya na zaman lafiya, wanda na farko a yi shi ne a birnin maskat na kasar Oman na biyu kuma a birnin Janeva na Swiss.
kuma wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da Amurka take ci gaba da tura makamai yankin har ma kusa da iran inda ta tura manyan jiragen yaki guda biyu da sauran Naurorin kakkabo makamai masu linzami.