Ministocin harkokin wajen Iran da Oman sun tattauna kan abubuwan da dake faruwa a yankin, musamman a Yemen.
A cewar IRNA, Sayyed Abbas Araghchi da Badr Al-Busaeidi sun yi magana don samar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin, inda suka tabo halin da ake ciki a yankin musamman a Yemen, makwabciyar Oman.
A cikin kwanaki biyu da suka gabata, ministan harkokin wajen Iran ya kuma gana da takwarorinsa na Turkiyya, Masar, Iraki, Saudiyya, da Oman don a kokarin da ake yi na rage tashin hankali a yankin.
Tattaunawar ta su dai na zuwa ne a daidai lokacin da Kasahen duniya ke ci gaba da mayar da martani kan rikicin da ya barke tsakanin Saudiyya da Yemen.
Ko a ranar Larabar nan ‘yan Houthi a Yemen sun dauki alhakin kai hari kan kamfanin mai na Saudiyya Aramco da ke Dhahran, a gabashin masarautar, da kuma filin jirgin sama da kuma matatar mai a babban birnin Riyadh, ba tare da bayyana ranar ba.
“Ayyukan zasu ci gaba cikin tsakiyar Saudiyya a cikin kwanaki masu zuwa, inda za a kai hari kan filayen jiragen sama da wuraren mai na makiya, kuma sakamakon zai yi tsanani,” in ji mai magana da yawun sojojin Yemen, Yahya Saree.