Iran da Oman sun kuduri aniyar fadada huldar dake a tsakaninsu

Kasashen Iran da Oman sun kudiri anniyar fadada huldar dake a tsakninsu. Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Massoud Pezeshkian, ya jaddada muhimmancin fadada alaka da

Kasashen Iran da Oman sun kudiri anniyar fadada huldar dake a tsakninsu.

Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Massoud Pezeshkian, ya jaddada muhimmancin fadada alaka da kasashen makwabta.

Ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da ministan harkokin wajen kasar Oman dake ziyara a Tehran.

Shugaba Pezeshakian, ya bayyana cewa wannan yana haifar da yanayi mai kyau don hanzarta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka sanya wa hannu tsakanin kasashen biyu don fadada dangantakar Tehran da Muscat.

“Iran ta kuduri aniyar aiwatar da yarjejeniyoyin kasashen biyu da faɗaɗa alaka da Oman a dukkan fannoni na moriyar juna in ji Massoud Pezeshkian.

Yayin da ya tabo abubuwan da suke faruwa kwanan nan a yankin da kuma duniya, da kuma rawar da Amurka da ‘yan sahayoniya suka taka wajen kawo cikas ga zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tsaro a duniya, ya kara da cewa: “Kokarin da Amurka da gwamnatin Sahoyoniya suka yi duk an yi su ne don kunna wutar yaki da kuma haifar da rashin tsaro, domin hana hadin kai tsakanin kasashen Musulmi da kuma haifar da rashin jituwa, ta haka ne za su tabbatar da muradun kansu da kuma cimma munanan manufofinsu.”

A nasa bangaren, Ministan Harkokin Wajen Oman ya bayyana gamsuwarsa da ganawa da Shugaba Pezeshkian kafin ya isar da gaisuwar Sarkin Oman ga gwamnati da al’ummar Iran, ya kuma bayyana fatansa na aiwatar da wadannan yarjejeniyoyin da kuma cimma sabbin damammaki na hadin gwiwa ta hanyar mu’amala da hadin gwiwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted