Iran da Nijar sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa

Kasashen Iran da Nijar sun gudanar da taron kwamitin hadin gwiwa kan tattalin arziki. An gudanar da taron ne a gefen taron baje koli na

Kasashen Iran da Nijar sun gudanar da taron kwamitin hadin gwiwa kan tattalin arziki.

An gudanar da taron ne a gefen taron baje koli na Iran 2025, karo na bakwai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda aka fara a birnin Tehran a ranar Litinin.

Mohammad Atabak, ministan masana’antu, ma’adinai, da kasuwanci na Iran; da Mohammad Ali Dehghan Dehnavi, shugaban kungiyar bunkasa kasuwanci ta Iran; da Sahabi Oumarou, ministan mai na Nijar, ne suka halarci taron.

Da yake jawabi a wajen taron, Atabak ya ce, bayan shafe shekaru 13 da aka shafe ana aikin kwamitin hadin gwiwa tsakanin Iran da Nijar,  “Muna fatan inganta dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashenmu biyu ta hanyar wannan takardar hadin gwiwa.”

Dehghan Dehnavi ya jaddada cewa, an gudanar da tattaunawa mai zurfi a cikin kwanaki biyun da suka gabata, inda masana suka yi nazari tare da musayar wasu tanade-tanade na hadin gwiwa tsakanin Iran da Nijar.

Ya ci gaba da cewa kwararrun da suka halarci taron sun amince da ci gaba da yin hadin gwiwa tsakanin Iran da Nijar a bangarori da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments