Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta sanar da cewa ta cimma matsaya da kasashen turan nan guda uku da aka fi sani da E3, komawa tattaunawa kan batun dage takunkumin da aka kakabawa kasar.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ne mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ne ya sanar da hakan inda yake cewa, Iran da kasashen Turai da suka hada da Faransa, Jamus da Birtaniya, sun amince da komawa teburin tattaunawa kan dage takunkumin da aka kakabawa kasar bayan an yi zaman shawarwari karo na uku da kasashen a Geneva.” Jiya Litini Inji Kazem Gharibabadi. “
” tattaunawar inji shi ta kasance mai mahimmanci, cikin gaskiya kuma mai ma’ana’’.
Mun yi aiki da wasu bayanai kuma mun tattauna a bangarori guda biyu na sassauta takunkumi da kuma batutuwan da ke da mahimmanci don cimma yarjejeniya,” in ji shi.
Bangarorin sun kuma yi musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi halin da ake ciki a yankin.
Taron na Geneva ci gaba ne na tattaunawar da aka yi da kasashen uku a watan Satumba a gefen taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York da kuma tattaunawar da aka yi a Geneva a watan Nuwamba.
Tun shekarar 2021 ne bangarorin biyu ke ci gaba da gudanar da tattaunawa, shekaru uku bayan da Amurka ta yi fatali da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, tare da laftawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tsauraran takunkumai, kuma duk wani yunkuri na kasashen turan na maida da Amurka cikin yarjejeniyar ya cutura.