Iran, da kasashen Turai sun amince da ci gaba da tattaunawa ‘nan gaba

Iran ta ce nan gaba kadan zata ci gaba da tattaunawa da kasashen turai kan shirinta na nukiliya bayan tattaunawarsu a jiya. Wani babban jami’in

Iran ta ce nan gaba kadan zata ci gaba da tattaunawa da kasashen turai kan shirinta na nukiliya bayan tattaunawarsu a jiya.

Wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce Tehran da kasashen Faransa, Jamus da Biritaniya – sun amince su ci gaba da tattaunawa “nan gaba kadan” bayan tattaunawar Geneva.

Kazem Gharibabadi, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin shari’a da harkokin kasa da kasa, ya ce tawagar Iran ta sake yin wani zagaye na tattaunawa da kasashen Turai uku, wanda aka fi sani da E3 a ranar Juma’a.

Ya kara da cewa, bangarorin sun tattauna tare da yin nazari kan ci gaban da aka samu a baya-bayan nan, na shiyya-shiyya da na kasa da kasa, musamman batun nukiliya da batun dage takunkumi.

Jami’in diflomasiyyar na Iran ya jaddada cewa: “Mun dage sosai wajen biyan bukatun jama’armu, kuma abin da muka fi so shi ne hanyar tattaunawa da mu’amala.”

A ranar Alhamis, Enrique Mora, mataimakin babban sakataren hukumar kula da harkokin waje ta Turai, ya tattauna a Geneva tare da Gharibabadi da Majid Takht Ravanchi, mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin siyasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments