Iran da wasu kasashen yankin Tekun Fasha sun yi Allah wadai da sabon kutse da farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta kasa da kuma ta sama a birnin Beit Jinn da ke kudancin Siriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 13, ciki har da yara.
A cikin wata sanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya jaddada ‘yancin da kasashen Yammacin Asiya ke da shi na kare ‘yancinsu da kuma ‘yancin yankinsu daga harin Isra’ila.
Ya kuma soki rashin daukar matakin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan take ‘yancin kai na kasashen yankin, musamman Siriya da Lebanon.
A nata bangaren, Qatar ta yi gargadin cewa wannan “yana kara ta’azzara tashin hankali kuma yana kawo cikas ga kokarin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin.”
Ita ma Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya, ta “yi Allah wadai da harin ” da sojojin Isra’ila ke yi, wadanda ke kokarin “wargaza tsaro da zaman lafiyar Siriya da mutanenta.”
Ma’aikatar Harkokin Wajen Kuwait ta kuma yi Allah wadai da harin: “Waɗannan hare-haren laifuka ci gaba ne na dabarun wargaza zaman lafiya, wanda ke barazana ga tsaro da kwanciyar hankalin yankin.
” Akalla ‘yan Siriya 13, ne suka mutu, yayin da wasu sama da 20 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ta kai a Beit Jinn, wani yanki na birnin Damascus.