Mataimakin ministan harkokin wajen mai kula da hakokin shari’a Kazem Gharibadabi ya sanar da cewa Iran da kasashe uku na turai Birtaniya, Jamus, da Farasna sun yarda da cewa za a ci gaba da tattaunawa akan batun daukewa Iran din takunkumi.
Gharibadabi ya ce; “An yi zama karo na uku na tattaunawa a tsakanin Iran da kasashen turai din a birnin Geneva, kuma tattaunawa ce da aka yi ta keke da keke,kuma ta haifar da da, mai ido.”
Gharibabadi ya kuma rubuta a shafinsa na X cewa: Mun tattauna tare da yin musayar ra’ayoyi a cikin fagage biyu da su ne, batun dauke takunkumi da kuma batun shirin Nukiliyar Iran na zaman lafiya.”
Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce an cimma matsaya ta baidaya akan cewa za a cigaba da tattaunawar domin kai wa ga cimma matsaya.