Iran da E3 sun kuduri aniyar bin hanyoyin diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar Iran

Iran da kasashen turan nan guda uku sun da ake wa lakabi da E3 sun kudiri anniyar bin hanyoyin diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar kasar

Iran da kasashen turan nan guda uku sun da ake wa lakabi da E3 sun kudiri anniyar bin hanyoyin diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar kasar ta Iran.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa, Iran da kasashen Turan uku Birtaniya da Faransa da Jamus (EU-3) sun kuduri aniyar yin amfani da diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.

Gharibabadi ya bayyana hakan ne a shafinsa na X bayan ganawarsa da wakilan kasashen Turan uku na yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015 a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-Ravanchi shi ma ya halarci taron.

Ya ce, wakilan Iran da daraktocin siyasa na EU-3 sun yi musayar ra’ayi tare da tattauna halin da ake ciki na shawarwarin nukiliya tsakanin Iran da Amurka da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata.

Ya ce Iran da EU-3 za su sake haduwa, idan akwai bukata, don ci gaba da tattaunawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments