Kasashen Iran da kuma Sin sun kudiri anniyar fadada dangantakar dake a tsakaninsu a dukkan fagage.
Bangarorin sun kuma bayyana damuwa game da halin da ake ciki a gabas ta tsakiya da yammacin asiyya.
Wannan bayyanin ya fito ne bayan ganawar data wakana tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghci da shi da takwaransa na Sin Wang Yi.
A yayin tattaunawar, Mista Yi ya bayyana cewa ya kamata kasar Sin da Iran su yi aiki kafada da kafada wajen kara ingancin amfani da tsarin hadin gwiwar na kasashen gungun BRICS” da kuma kula da muradun kasashe masu tasowa.
Ya kuma kara da cewa, a yanayi na rashin tabbas da ake kaka-ni-ka-yi a ciki a duniyar yau.
“Iran da Sin, a matsayinsu na abokan huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, sun kuduri aniyar fadada tuntubar juna ta kut-da-kut, da nufin zurfafa huldar dake tsakaninsu domin moriyar jama’arsu, da kara ba da gudummawa wajen bin doka da oda a matakin kasa da kasa, da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.” ” a cewar ministan harkokin wajen Iran.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kuduri aniyar yin amfani da hadin gwiwar da ke tsakaninta da kasar Sin, tana mai kallon shirin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare na shekaru 25 a matsayin wani ginshiki mai karfi na inganta dangantakar dake tsakanin bangarori daban daban.