Iran Da Afirka Ta Tsakiya  Za Su Yi Aiki Tare Ta Fuskar Ma’adanai

Ministan kanana da matsakaitan kamfanoni na kasar Afirka Ta Tsakiya  ya bayyana cewa kasarsa a shirye take, ta yi aiki da jamhuriyar musulunci ta Iran

Ministan kanana da matsakaitan kamfanoni na kasar Afirka Ta Tsakiya  ya bayyana cewa kasarsa a shirye take, ta yi aiki da jamhuriyar musulunci ta Iran a fagen hako da sarrafa ma’adanai.

Ministan kananan masana’antun na kasar Afirka Ta Tsakiya wanda ya halarci “Baje Kolin Kere-keren Iran na 2024.”

Ministan kananan masana’antun na kasar Afirka Ta Tsakiya ya kuma kara da cewa, kasar tasa tana cikin shirin bai wa Iran dammar gina masana’antu na sarrafa ma’adanai,domin a kasar tasa da akwai nau’o’i, mabanbanta 400 na ma’adanai da ya zuwa aka gano,domin haka da akwai bukatar yin aiki a tare da Iran.

A kowace Shekara Iran tana shirya baje kolin kayan da take kerawa domin nunawa duniya, da kuma samo hanyar bunkasa alaka da kasashe.

A yayin baje kolin da a halin yanzu yake cigaba, kasashe an sami halartar baki daga kasashe da dama da su ka  hada da nahiyar Afirka. .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments