Iran Da Afganistan Sun Tattauna Al-Amura Masu Muhiammaci A Kabul

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi  wanda ya jagoranci tawagar yan siyasa da kuma tattalin arzikin kasarsa zuwa birnin Kabul babban birnin kasar Afganistan,

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi  wanda ya jagoranci tawagar yan siyasa da kuma tattalin arzikin kasarsa zuwa birnin Kabul babban birnin kasar Afganistan, a yau Lahadi sun tattauna al-amura masu muhimmanci  tsakaninsu da kuma yanking aba daya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa ministan ta hadu da tokwaransa na rikon kwarya Amir Khan Muttaki a birnin Kabul inda suka tattauna al-amura da suka shafi kasashen biyu. Wadanda suka hada da al-amuran kan iyakokin kasashen biyu, tsaro, ruwa da hakkin ko wace kasa kan ruwan da ke kwarara daga kasar Afganistan zuwa kasar Iran. Da batun miliyoyin yan kasar Afgansitan wadanda suke rayuwa a kasar Iran na shekaru kimani 50.

Ministocin biyu sun tattauna al-amura da suka shafi kasashen biyu, wadanda suka hada da makobtaka, musulunci, al-adu da sauransu. Kasashen biyu malobta ne na shekaru aru-aru.

A nashi bangaren Muttaki ya godewa kasar Iran kan daukar bakwantan miliyoyin yan kasar Afganistan, ya kuma bayyana cewa gwamnatin Taliban tana iya kokarinta don ganin sun dawo gida musamman ganin cewa al-amura sun fara kyautata a kasar.

Sannan daga karshe ya ce kasashen biyu zasu yi aiki tare don yaki da yan ta’adda a kasashen biyu musamman a kan iyakokin kasashen biyu

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments