Sanarwar hadin gwiwa da Iran, China, da Rasha suka fitar ya bayyana cewa: Matakin da kasashen yamma suka dauka a Hukumar Gwamnonin IAEA ba shi da tushe a shari’a
An amince da kudurin da Amurka da Tarayyar Turai (Birtaniya, Faransa, da Jamus) suka gabatar kan shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a wani taron Kwamitin Gwamnonin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA).
Kudirin da aka zartar na adawa da Iran, wanda aka zartar da shi da kuri’u 23 na masu goyon baya, kuri’u 8 na wadanda suka ki kada kuri’a da kuma kuri’u 3 masu kin amincewa da kudurin, ya dogara ne akan maimaita zarge-zargen siyasa game da shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya na Iran, yin watsi da hadin gwiwar da Iran ke bayarwa ga Hukumar IAEA tare da yin watsi da sakamakon cin zarafin sojojin Amurka da Isra’ila kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran da ke karkashin tsarin sa idon Hukumar ta IAEA.
A cewar wani rahoto na Reuters, kudurin ya bukaci Darakta Janar na IAEA da ya mika sabon kuduri da kudurorin da aka ambata a baya a cikin rubutunsa, da kuma rahotonsa na baya-bayan nan game da Iran ga kasashe mambobin IAEA, Kwamitin Tsaro, da Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Tun da farko dai, Iran, China, da Rasha sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa da ke adawa da matakin siyasa da Amurka da kasashen Turai uku suka dauka na mika batun shari’ar Iran ga kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya saboda rashin damar shiga cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran.
Sanarwar hadin gwiwa ta ce: “Batun tura takaddamar Iran zuwa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ba shi da tushe na shari’a, kuma yana da nufin kara ta’azzara lamarin, sannan ya saba wa alkawarin da masu fitar da sanarwar suka yi na bin hanyar diflomasiyya.”