Cibiyar nazari da bincike ta majalisar shawarar musulunci ta Iran ta bayyana cewa; Ma’adanin alminiun yana a matukar muhimmanci saboda amfanin da yake da shi a fagen tattalin arzikin duniya.Shugaban cibiyar Dr. Nagahdari ya fada a yau Litinin cewa; Ma’adanin na alminium yana da matukar muhimmanci, kuma wanda ake da shi a Iran zai zama ana sarrafa shi da yin kere-kere da shi domin fitarwa waje saboda samun kudaden shiga.
Shugaban cibiyar da nazarin a Malalisar shawarar musulunci ta Iran, ya gabatar da jawabi ne a wurin taron kere-kere da ake yi da alminium, yi kira da a rika fitar da kayan da aka sarrafa, maimakon a fitar da danyansa zuwa kasuwannin duniya.
Haka nan kuma ya ce; A cikin shekaru biyu na bayan na an sami karuwar saffara alminium a duniya, inda ya tashi daga ton miliyan 15 zuwa ton miliyan 33 a kowace shekara.
Nigahdari ya kuma yi Ishara da yadda a Iran ake da dandazon al’minium kwance a kasa da ya kai ton miliyan 23, wanda yake a matsayin kaso 2.3% na alminium din da ake da shi da duniya baki daya. Hakan ya mayar da Iran din zama ta goma a cikin jerin kasashen da Allah ya huwacewa wannan ma’adani.
A cikin Iran ana sarrafa da samar da kayan dunkulalliyar sandar wutar lantarki ( cathod) wacce aka kera da al’minium da kaso 90% da ake da bukatuwa da ita, kamar yadda Nigahdari ya bayyana.