Iran: Babu Batun Tattaunawa Har Sai Amurka Ta Samar Da Aminci

kasar Iran tace babu batun tattaunawa har sai kasar Amurka ta samar da amince da zaa iya yarda da shi

babban sakataren kolin tsaron kasa major ganaral Mohsen Rezai ya jaddada cewa babu wani batun tattaunawa tsakanin su da kasar Amurka har sai  ta dauki matakin da tabbatar da gaskiyarta, kuma matakin zai fara ne da cika dukkan sharuddan da iran ta gabatar

A watan da ya gabatar babban jami’in tsaron ya bayyana cewa Tehran ta aike da sharudda 7  ga kasar Amurka  ta hanyar mai shiga tsakani na kasar Qatar, kuma suna jiran shugaban amurka Donald trump ya bada amsa akai, sharadin mu shi ne kawo karshen yaki a dukkan bangarori,da kuma sakin kadarorin iran da ake rike, da kuma kawo karshen killawar da akayi ta ruwa, yace martanin Washington kan wadannan batutuwa bai isa ba

haka zalika yace a lokain ziyarar da babban hafsan sojin kasar Pakistan Asim munir ya kawo birnin Tehran a jiya talata ya nuna cewa alumma da gwamnatin iran kansu a hade yake yadda ya zama babu wata tataunawa da za ta gudana ba tare da amurka ta tabbatar da gaskiyarta akan lamarin ba.

Riza’I ya wallafa a shafinsa na X cewa babu digo daya na yuraniyom da aka tace da zai fita daga  iran, kuma yayi watsi da bukatun da jami’an amurka daban daban suka yi ta gabatarwa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted