Iran Ba Zata Karbi Umrni Daga Wani Kan Shrin Nukliyar Kasar Ba

Mohammad Reza Aref mataimakin shugaban kasa na farko a nan JMI ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata karbi umurni daga wata kasa dangane

Mohammad Reza Aref mataimakin shugaban kasa na farko a nan JMI ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata karbi umurni daga wata kasa dangane da shirin makamashin nukliya ta zaman lafiya na kasar ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Aref yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa, JMI ta na ci gaba da jajircewa da takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dora mata, dangane da shirin kasar na amfani da fasahar Nukliya.

Sai dai har yanzun ba zata nemi shawara ko karbi umurni daga wata kasa a kan amfani da wannan fasaha mai dimbin amfani ba.

Mataimakin shugaban kasar ya ce, sinadarin Nukliya ya na da matukar amfani kuma mai yawa, bai kamata a haramtawa wasu kasashe amfani da shi ba.

Banda haka ya ce, fasahar nukliya ci gaba ne, idan an hada tsarin  addinin musulunci da ke gudanar da kasar, ci gaba ne mai yawa. Yace kasar Iran tana da arziki mai yawa tare da wadannan abubuwa biyu.

Yace ammam wasu kasashe a duniya suna sun su takaita wannan fasahar garesu su kadai, don su rika bautar da mutane. Basa son ganin Iran ta kai ga wannan fasahar, don haka sun samar da ra’ayin kin iraniyawa a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted