Iran Ba Za Ta Taba Tattaunawa Akan Makamanta Masu Linzami Ba

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci wanda ya halarci taron shekara-shekara na “Aljazira a birnin Doha na kasar Qatar, ya fadawa tashar talbijin din cewa;

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci wanda ya halarci taron shekara-shekara na “Aljazira a birnin Doha na kasar Qatar, ya fadawa tashar talbijin din cewa; Tattaunawar da aka bude da Amurka ta yi kyau, a matsayin masomi, amma da akwai hanya mai tsawo kafin akai ga cimma gaci.”

Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kuma ce; Tattaunawar da aka yi ta bayan fage ce, kuma batun tace sanadarin Uranium wani hakki ne na Iran, kuma dole ne zai ci gaba.

Dangane da batun makamai masu linzami na Iran kuwa, Abbas Arakci ya ce; Hatta a lokacin yaki ma, sun kasa rusa makaman na Iran.

Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya ce Iran a shirye take ta kulla yarjejeniya akan batun shirinta na Nukiliya na zaman lafiya.

Bugu da kari, ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya ce; Ta hanyar tattaunawa ce kadai za a iya warware batun makamashin Nukiliyar Iran.

Dangane da yiyuwar kawo wa Iran hari kuwa, ministan harkokin wajen na Iran ya ce; Idan aka kawo wa Iran hari, Iran za ta kai wa sansanonin Amurka dake wannan yankin hari.

Haka nan kuma ya ja hankalin kasashen da Amurka take da sansanoni a cikinsu da cewa, da akwai banbanci a tsakanin kai wa sansanonin Amurka hari da kuma ace su aka kai wa harin.

A jiya Juma’a ne dai aka bude tattaunawa a tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma Amurka a kan shirinta na makamashin Nukiliya a birnin Mascut na kasar Oman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted