Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi zai gana da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi a wannan mako domin kammala sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwa.
Ganawar za ta iya kawo sauyi wajen tattaunawar diflomasiyya kan batun nukiliyar Iran, da kuma da sassauta matsin lambar da kasashen Turai ke yi game da shirinta na nukiliyar Iran da kuma yunmkurinsu na neman dawo da takunkuman MDD kan Iran.
Bayyanin da shafin yanar gizo na Iranpress ya rawaito ya ce mai yi wa ganawar tsakanin Araghchi da Grossi, ta wakana a lokacin ziyarar ministan harkokin wajen Iran a Alkahira, babban birnin Masar, a kan hanyarsa ta zuwa Tunisiya.
Zai kuma iya zama mataki na karshe kuma mafi mahimmanci a cikin makonnin da aka shafe ana tattaunawa mai zurfi kan ayyukan hukumar ta IAEA a Iran.
Dangantaka tsakanin Iran da kuma hukumar makamashin nukliya ta duniyar ta yi tsami ne bayan harin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran.