Iran: An Nada Sabbin Kwamandojin Rundunar “Khatamul-Anbiya” Na Tsaron Sararin Samaniya

A karkashin umarnin babban kwamandan rundunar sojan kasar Iran, an nada sabbin kwamandojojin rundunonin hadin gwiwa na tsaron sararin samaniya na “Khatamul-Anbiya” tare da sojojin

A karkashin umarnin babban kwamandan rundunar sojan kasar Iran, an nada sabbin kwamandojojin rundunonin hadin gwiwa na tsaron sararin samaniya na “Khatamul-Anbiya” tare da sojojin kasa.

An nada Laftanar kasar Ali Ridha Ilhami a matsayin babban kwamandan rundunar “Khatamul-Anbiya” ta tsaron sama, da kuma cibiyar hadin kai ta tsaron sararin samaniya da sojojin kasa.

Shi kuwa Kanar Bahman Bahmard, an nada shi ne a matsayin kwamandan sojan sama na rudunar sojojin kasa.

A wurin bikin nadin, an girmama tsofaffin kwamandoji da su ka hada Laftanar kanar Hamid Wahidi, da shi ne kwamandan sojan sama da laftanar Ali Riza Sabahi Fard, kwamandan rundunar ta “Khatamul-Anbiya”.

Daga cikin wadanda su ka halarci wannan bikin da akwai kwamandan rundunar sojan kasa,janar Amir Hatami, da laftanar  Amind Muhammad Shirazi” shugaban ofishin babban kwamandan rundunar sojan kasa, sai kuma Laftanar kanar Haidari, wanda shi ne mataimakin kwamandan rundunar ta “Khatamul-Anbiya”. Sai babban hafsan hafsoshin sojan kasa  Admiral Habibullah Sayyari..

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted