Iran : Wasu Fitattun Alkalai 2 Sunyi Shahada A Wani Harin Ta’addanci

Ma’aikatar shari’a a Iran, ta sanar da shahadar wasu manyan alkalai guda biyu na kasar a wani harin ta’addanci da aka kai musu a cikin

Ma’aikatar shari’a a Iran, ta sanar da shahadar wasu manyan alkalai guda biyu na kasar a wani harin ta’addanci da aka kai musu a cikin kotun kolin kasar dake Tehran.

A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta bayyana sunayen alkalan da suka hada da Ali Razini, shugaban reshe na 39 na kotun da kuma Mohammad Moqiseh, shugaban reshe na 53.

Bayanai sun ce wani dan bindiga ne ya harbe manyan alkalan a ofishinsu, sannan ya jikkata wani alkalin da dogari kafin daga bisani ya hallaka kansa.

Saidai ba’a kai ga sanin ainahin dalilin dan bindigan na aikata wannan kisan ba in ji mai magana da yawun ma’aikatar, Asghar Jahangir.

Tuni shugaban kasar Massoud Pezeshkian, ya bayar da umurnin gudanar da bincike domin zakulo suwa ke da hannu a wannan ta’addancin.

Alkalan dai sun yi aiki kan shari’o’in yaki da laifukan da suka shafi tsaron kasa, leken asiri da ta’addanci.

A cewar binciken farko da aka yi, maharin ba ya da hannu a wasu kararraki da ke gaban kotun koli.

Alkali Razini, mai shekaru 71, ya rike mukamai da dama a bangaren shari’a na Iran, kuma a baya ya fuskanci wani yunkurin kisan gilla a shekarar 1998 daga wasu mahara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments