Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya ce Amurka da Birtaniyya na da hannu a mummunar aika-aikar da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka aikata a sansanin al-Nuseirat da ke tsakiyar yankin zirin Gaza.
Da yake magana a taron manema labarai na mako-mako a ranar Litinin, Nasser Kan’ani ya sake yin Allah wadai da kisan gillar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a sansanin al-Nuseirat, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula 274 Falasdinawa tare da jikkata wasu 698.
“Dole ne kasashen duniya su sauke nauyin da ya rataya a kansu na hakkin shari’a domin kawo karshen laifuffukan da Isra’ila take aikatawa, tare da daukar kwararan matakai domin ganin an tilasta haratacciyar kasar ta yi biyayya ga dokoki da ka’idiji na kasa da kasa, ” in ji shi.
Sojojin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a ciki da wajen sansanin ‘yan gudun hijira na Deir el-Balah da Nuseirat a ranar Asabar kafin su kwato wasu yahudawan Isra’ila hudu da aka yi garkuwa da su.
Sun kaddamar da farmakin ne da tsakar rana, suna masu ikirarin kai hari kan kayayyakin aikin soji da ke sansanin a wani bangare na “aikin ceto” amma shaidu da ‘yan jarida da ke wurin sun ce Isra’ila ta yi ruwan bama-bamai a kan gidajen jama’a da kuma wuraren da aka tsugunnar da daruruwan mutanen ad suka kauracewa muhallansu, lamarin da ya janyo hasarar rayuka masu yawa.