Babban kwamandan sojojin kasa na JMI Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin JMI a shirye suke su maida martani ko kuma kai hari kan makiya a duk lokacinda suka takali kasar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hatami yana fadar haka a bikin kaddamar da jiragen ruwan yaki masu suna Sahand da kuma Kurdestan a yau Asabar.
Janar Hatami ya bayyana cewa tsarin tsaro a JMI shi ne kare kai da kuma hana kai hare-hare.
Hatamiya ce ‘wannan yana nufin ba zamu jira sai an kawo mana hari ba, idan ya tabbata a garemu makiya suna kokarin kawo mana farmaki, muna iya hana su hakan tun basu kawo ba.
Dangane da yakin shekaru 8 masu tsarki babban kwamandan ya ce Iran zata ci gaba da kasancewa kasa mai karfi wajen kare kanta sannan zata maida al-amuran tsaro a yankin al-amarinta.
Ya ce: a wannan zamanin, ba’aa bambantawa tsakanin tsaron kasa da kuma tsaron yanki. Saboda duk abinda yake faruwa a yankin da kuke rayuwa tabba zai shafi kasar da kake rayuwa a cikinta.