Search
Close this search box.

Iran A Shirye Take Ta Fadada Dangantaka A Dukkan Fagage Da Kasar Venezuela

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya kara jaddadawa shugaban kasar Venezuela kan cewa gwamnatinsa a shirye take ta kara fadada dangantaka da kasashen Laten Amurka

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya kara jaddadawa shugaban kasar Venezuela kan cewa gwamnatinsa a shirye take ta kara fadada dangantaka da kasashen Laten Amurka musamman kasar Venezuela.

Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka ne a zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Venezuela Necolas Madoro a jiya Litinin.

Labarin ya kara da cewa shugaba Pezeshkiyan ya taya shugaba Madoro nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a cikin yan kwanakin da suka gabata. Ya kuma bayyana cewa JMI tana goyon bayan kasar Venezuela, tana kuma yin allawadai da shishigin da wasu kasashe suke yi a cikin al-amuran cikin gida na kasar ta Venezuela.

Daga karshe Pazeshkiyan ya bukaci a gaggauta aiwatar da yarjeniyoyin da ke tsakanin kasashen biyu. Ya kuma bayyana cewa Iran a shirye take ta yi aiki da kasar Venezuela a bangaren makamashi, fasahar kere kere, man fetur da sauransu.

A nashi bangaren shugaban kasar Venezuela Nicolas Madoro ya bayyana cewa kasar Venezuela tana bukatar fadada dangantaka da kasar Iran don samun ci gaba a dukkan bangarori.

Ya kuma taya shugaba Pezeshkiyan munar zabensa a matsayin shugaban kasar Iran, sannan ya bayyana cewa rigingimun da suka faru bayan zabensa a kasar, shishigi ne na HKI da Amurka don maida kasar Venezuela baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments