Iran A Shirye Take Ta Bada Dama A Gudanar Da Bincike A Cibiyoyin Nukliyar Kasar

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa kasar Iran tana gudanar da ayukanta na bincike a cibiyoyin Nukliyar kasar tare amincewa da bincike kuma

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa kasar Iran tana gudanar da ayukanta na bincike a cibiyoyin Nukliyar kasar tare amincewa da bincike kuma a bayyana take hakan.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto shugaban yana fadar haja a jiya Asabar a lokacinda yake ganawa da mataimakin firay minister kuma ministan harkokin wajen kasar Kazakistan Murat Abugaliuly  wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran.

Shugaban ya kara da cewa tun lokacinda kasar ta fara tache sinadarin Uranium hukumar makamacin Nukliya ta duniya IAEA na sanya ido a ayyukanta, sannan tun lokacin bata bada rahoton cewa shirin nata ba ta zaman lafiya ba.

Daga karshe shugaban ya kara da cewa bayan wannan kuma ba zamu taba amincewa wani ya hanamu hakkin sarrafa makamashin nukliya na zaman lafiya ba. Don haramtawa mutanemmu amfani da wannan fasahar mai muhimmanci a rayuwarsu.

Yace a dai-dai lokacinda Iran tana barin a gudanar da bincike a cikin ayyukanta, ba zata bawa wani damar fayyace makomar al-ummarmi da ra’ayinsa ba, inji shugaban.

Ya kammala da cewa JMI a shirye take ta shiga tattaunawa na hankali a kan shirin na makamashin Nukliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments