Rundinar kare juyin juya hali musulinci ta iran, ta sanar da kaddamar da jerin sabbin hare hare karo na 94 kan sansanonin Amurka a yankin dama na sojojin gwamnatin Isra’ila.
Hare haren sun shafi Cibiyoyi da sansanonin sojojin ‘yan sahayoniya a kudanci, tsakiya da yankuna da isra’ila ta mamaye da kuma Tel-Aviv cewar sanarwar ta IRGC a wannan Asabar.
IRGC ta ce an yi amfani da wasu su’uman makamai irinsu Kheibar-Shakan, da makamai masu linzami dake amfani da makamashi mai yauni da kuma na mai, da ake tafiyar da su daga nesa da kuma wasu jiragai marasa matuka a jerin hare haren karo na 94 dake zaman martani ga yakin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan kasar.
Yankunan da suka hada da Dimona, Negev, Beersheba, Ramat Gan, sun fusknaci hare hare masu tsanani bayan da makamman garkuwa na isra’ilar suka kasa tabaka komai wajen cafko makamman.
Sanarwar ta kara da cewa ‘yan gwagwamarya daga Yeman, sun kai hare hare a kudancin yankunan da Isra’ila ta mamaye da makami mai linzami.
Haka zalika dakarun gwagwamarya a Iraki su ma sun kaddamar da hare hare da dama.
Sanarwar ta IRGC, ta kara da cewa da yardar Allah za’a dauki fansar jinin da aka zubar na wadanda aka zalinta a fadin duniya, musamman yara a Gaza, Lebanon, Yeman da Iraki da kuma wasu kasashen Musulmi.