Amurka da Isra’ila sun sake kai wa cibiyar makamashin nukiliyar Iran ta Bushehr hari

Harin na safiyar ranar Asabar, ya kuam lalata wani banagre na cibiyar ta Bushehr, saidai babu wata barna da aka samu a babban bangare na cibiyar wanda ya tsaida aikin cibiyar.
Fafaroma Leon na 14 ya bukaci a kawo karshen yaki a iran ta hanyar diflomatsiyya

fafaroman ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Isra’ila inda ya jadadda bukatar amfani da hanyoyin diflomatsiyya domin kawo karshen yakin da ake da iran.
Iran ta kaddamar da jerin hare-hare na 94 akan isra’ila da sansasonin Amurka a yankin

Hare haren sun shafi Cibiyoyi da sansanonin sojojin ‘yan sahayoniya a kudanci, tsakiya da yankuna da isra’ila ta mamaye da kuma Tel-Aviv cewar sanarwar ta IRGC a wannan Asabar.
Ana ci gaba da farautar matukin jirgin yakin Amurka da Iran ta kakkabo

Iran ta yi tanadin tukuici mai tsoka ga duk wanda ya cafko mata matukin jirgin yakin Amurka da sojojin kasar suka kakkabo a kasar.
Sama da jiragai marasa matuka 160 na makiya Iran ta kakkabo tun soma yakin Amurka da Isra’ila

Hedikwatar rundinar sojojin sama ta iran ta sanar da cewa sama da jiragai marasa matuka 160 ne ta kakkabo tun bayan soma yakin da Amurka da isra’ila suka kaddamar kan kasar.