Iraki : Jam’iyyar al-Soudani ta samu rinjaye a Majalisar dokoki

A Iraki an sanar da sakamakon karshe na zaben ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar Talata data gabata. Sakamakon ya nuna cewa Jam’iyar

A Iraki an sanar da sakamakon karshe na zaben ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar Talata data gabata.

Sakamakon ya nuna cewa Jam’iyar Firaminista Mai Barin Gado Mohamed Shia al-Soudani ce ta sami rinjaye mai yawa a majalisar da kujeru 46, inda za ta rike kusan rabin kujerun, idan aka kwatanta da kasa da kashi 40% a baya.

Majalisar za ta gudanar da zamanta na farko a watan Janairun 2026.

Sabuwar majalisar dokokin za ta kuma zabi sabon shugabanta daga bangaren ‘yan Sunni sai kuma shugaban Jamhuriya, wanda dole ne ya kasance daga bangaren Kurdawa.

Shi kuwa shugaban gwamnati wato firaminista dama dole ne ya fito daga bangaren ‘yan shi’a kamar tsarin mulkin kasar ta tanada a Iraki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments