Asusun Bayar Da Lamuni Na Duniya ( IMF) ya bayar da shawara ga gwmanatin tarayyar Nigeria akan kar ta sake dawo da tallafin man fetur.
Asusun bayar da lamunin na duniya ya ce; tallafawa man fetur yana da tsada sosai, kuma a mafi yawancin lokuta masu karfi ne suke amfana da shi ta hanyoyin da ba su dace ba. Haka nan kuma yana kara matsin lamba ta kudade a lokacin da yawan bashi yake karuwa.
Manaja mai kula da harkokin tafiyar da kudade a Asusun, ya bayyana hakan ne dai a yayin wani taron manema labaru da ya yi a kasar Thailand.
Wannan furucin na jami’in IMF ya biyo bayan matakin da gwamnatin tarayyar Nigeria ta dauka na rage farashin man fetur na tsawon wata guda.