Jami’an jihohi da na birane a Illinois da Minnesota sun shigar da karar hadin gwiwa a wannan Litinin kan gwamnatin Trump, suna masu ambaton cewa tura jami’an shige da fice zuwa yankunan Chicago da Minneapolis ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Amurka kuma ya keta haƙƙin jihohi.
Wannan matakin shari’a ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara samun tashe-tashen hankula da hare-haren da gwamnatin Trump ta amince da su, musamman ma a kan jihohin da ‘yan Democrat ke jagoranta.
Karar jihar Illinois na neman hana Hukumar Kwastam da Kare Iyakoki ta Amurka gudanar da aikin tabbatar da shige da fice a cikin jihar ba tare da izinin majalisa ba. Sai kuma ƙarar Minnesota ta buƙaci a kawo ƙarshen “ƙaruwar jami’an tarayya” da ba a taɓa gani ba a jihar.
An shigar da ƙarar jihar Minnesota, wadda jihar da biranen Minneapolis da St. Paul suka shigar, tana zargin cewa hare-haren jami’an ICE sun yi hannun riga da doka. Ƙarar ta yi iƙirarin cewa “dubban jami’an D.H.S. dauke da makamai sun mamaye Birane Biyu don gudanar da hare-haren da kuma kawo tsaiko da kama mutane masu haɗari, wanda kuma ana aiwatar da farmakin ba bisa ƙa’ida ba, da kuma aikata abubuwan da sun sabawa kundin tsarin mulki.”
Jami’an gwamnatin tarayya sun kare matakin da cewa ya zama dole don aiwatar da ajandar gwamnatin Trump kan shige da fice a yankunan da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi suka nuna turjiya.